Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.”

  2. Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.”

  3. Saboda haka Ahab ya kira sojoji matasa na shugabannin yankuna, mutum 232. Sa’an nan ya tattara sauran Isra’ilawa su 7,000 gaba ɗaya.

  4. Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin.

  5. Kwana bakwai suka yi sansani ɗaura da juna, a rana ta bakwai sai yaƙi ya haɗu. Isra’ilawa suka kashe sojojin kafa na Arameyawa dubu ɗari a rana ɗaya.

  6. Ya yi abar ƙyama ƙwarai ta wurin bin gumaka, kamar Amoriyawan da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ila.)

  7. Hazayel ya ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake kuka?” Elisha ya amsa, “Domin na san illar da za ka yi wa Isra’ilawa. Za ka ƙona biranensu masu katanga, ka karkashe majiya ƙarfinsu da takobi, ka fyaffyaɗe ƙananan yaransu da ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”

  8. Sai Ubangiji ya tā da mai ceto wa Isra’ila, suka kuma kuɓuta daga ikon Aram. Ta haka Isra’ilawa suka yi zama a gidajensu yadda suka yi a dā.

  9. Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, ya kuma damu da su saboda alkawarinsa da Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Har yă zuwa yau bai yarda yă hallaka su ko yă shafe su daga gabansa ba.

  10. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila har ya miƙa ɗansa hadaya a wuta, yana bin hanyoyin banƙyama na al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

  11. Duk wannan ya faru ne saboda Isra’ilawa sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fitar da su daga Masar daga ƙarƙashin ikon Fir’auna sarkin Masar. Sun yi wa waɗansu alloli sujada

  12. suka kuma bi gurbin al’umman da Ubangiji ya kora a gabansu, da kuma ayyukan da sarakuna Isra’ila suka gabatar.

  13. Isra’ilawa a ɓoye sun aikata abubuwan da ba daidai ba ga Ubangiji Allahnsu. Tun daga hasumiyoyi har zuwa birane masu katanga, sun gina wa kansu wuraren sujada na tudu a dukan garuruwansu.

  14. Isra’ila suka nace cikin dukan zunuban Yerobowam, ba su kuwa rabu da su ba

  15. Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu.

  16. Har yă zuwa yau, sun nace da ayyukansu na dā. Ba sa yin wa Ubangiji sujada, ba sa kuma bin dokoki da farillansa, dokoki da umarnan da Ubangiji ya ba wa zuriyar Yaƙub, wadda ya ba wa suna Isra’ila.

  17. Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.)

  18. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya bi munanan al’adun al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

  19. Amma mutanen ba su kasa kunne ba. Manasse ya ɓad da su, har suka yi muguntar da ta fi ta al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.

  20. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.

  21. Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.

  22. Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.

  23. Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.

  24. Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000.

  25. Sa’an nan Solomon ya tattara zuwa Urushalima dattawan Isra’ila, dukan kawunan kabilu da manyan iyalan Isra’ilawa, don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda.