Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. “Bawana Musa ya mutu. Yanzu sai ka tashi tare da mutanen nan duka, ku yi shirin ƙetare kogin Urdun zuwa cikin ƙasar da zan ba su Isra’ilawa.

  2. Aka gaya wa sarkin Yeriko cewa, “Ji fa, waɗansu Isra’ilawa sun shigo nan da dare don su leƙi asirin ƙasar.”

  3. Kashegari Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Shittim suka nufi Urdun inda suka sauka kafin su haye.

  4. Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku.

  5. Sai Yoshuwa ya kira mutum goma sha biyu da ya zaɓa daga cikin Isra’ilawa, ɗaya daga kowace kabila

  6. ya ce musu, “Ku je tsakiyar Urdun inda akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku yake. Kowannenku yă ɗauki dutse ɗaya a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilan Isra’ila,

  7. Sai ku ce musu, ruwan Urdun ya yanke a gaban akwatin alkawari na Ubangiji, a lokacin da akwatin alkawarin ya ƙetare Urdun. Waɗannan duwatsu za su zama abin tuni ga Isra’ilawa har abada.”

  8. Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.

  9. Mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse suka ƙetare da shirin yaƙi, suka wuce gaban Isra’ila kamar yadda Musa ya ce su yi.

  10. Ya ce wa Isra’ilawa, “Nan gaba in yaranku suka tambayi iyayensu suka ce, ‘Mece ce ma’anar waɗannan duwatsun?’

  11. To, da dukan sarakunan Amoriyawa na yammancin Urdun, da dukan sarakunan Kan’aniyawan da suke bakin teku suka ji yadda Ubangiji ya busar da kogin Urdun a gaban Isra’ilawa, har sai da dukansu suka ƙetare, zuciyarsu ta narke, suka karaya sosai har ma suka rasa samun ƙarfin hali su fuskanci Isra’ilawa.

  12. A lokacin nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu ka yi wa Isra’ilawa kaciya.”

  13. Sai Yoshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa Isra’ilawa kaciya a Gibeyat-Ha’aralot.

  14. Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka.

  15. Da yamman rana ta goma sha huɗu ga wata, lokacin da suke a Gilgal a filin Yeriko, Isra’ilawa suka yi Bikin Ƙetarewa.

  16. Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, Manna ta yanke, mutanen Isra’ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan’ana.

  17. Ƙofofin Yeriko kuwa a kulle suke ciki da waje saboda Isra’ilawa, ba mai fita babu kuma mai shiga.

  18. Amma Isra’ilawa ba su yi aminci game da kayan da aka hallaka ba; Akan ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera, na kabilan Yahuda ya kwashi waɗansu abubuwa, saboda haka fushin Ubangiji ya sauka a kan Isra’ilawa.

  19. Shi ne ya sa Isra’ilawa suka kāsa yin tsayayya da abokan gābansu; suka juya suka gudu domin za a hallaka su. Ba zan sāke kasancewa tare da ku ba sai in kun hallaka duk abin da aka keɓe don hallaka.

  20. Suka kwashe kayan daga tenti ɗin suka kawo wa Yoshuwa da sauran Isra’ilawa, suka baza su a gaban Ubangiji.

  21. kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra’ilawa. Ya gina bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Littafin Dokoki na Musa, bagade na duwatsun da ba a sassaƙa su ba, waɗanda ba wani ƙarfen da ya taɓa su. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kai.

  22. A can, a gaban Isra’ilawa, Yoshuwa ya rubuta dokokin Musa a kan duwatsun.

  23. Saboda haka Isra’ilawa suka tashi a rana ta uku suke je biranen mutanen, wato, Gibeyon, Kefira, Beyerot da Kiriyat Yeyarim.

  24. Amma Isra’ilawa ba su kai musu hari ba domin shugabanninsu sun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane Isra’ila duka kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.

  25. Yoshuwa kuwa ya cece su daga hannun Isra’ilawa, har ba su kashe su ba.