Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Young Men

347 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amsa da take ta gaskiya tana kamar sumba a leɓuna.

  2. Ka gama aikinka ka kuma shirya gonakinka; bayan haka, ka gina gidanka.

  3. Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba, ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.

  4. Kada ka ce, “Zan yi masa kamar yadda ya yi mini; zan rama abin da wannan mutum ya yi mini.”

  5. Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;

  6. ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe.

  7. Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.

  8. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,

  9. sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.

  10. Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya; zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini.

  11. Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari, amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya.

  12. Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa.

  13. Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya mahaifiyarsa ta koya masa,

  14. “Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina! Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!

  15. Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata, ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna.

  16. Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’

  17. Za a binne shi kamar jaki za a ja shi a ƙasa a jefar a bayan ƙofofin Urushalima.”

  18. “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka, bari a ji muryarka a Bashan, yi kuka daga Abarim, gama an murƙushe dukan abokanka.

  19. Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba.

  20. To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”

  21. Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”

  22. Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,

  23. ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”

  24. Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?”

  25. Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”