Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Second Coming of Christ

144 ayoyi · 65 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.”

  2. Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu.

  3. yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi.

  4. Yanzu fa, ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu iya tsaya gabagadi babu kunya a dawowarsa.

  5. Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.

  6. Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi.

  7. Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa

  8. don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.”

  9. To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki.

  10. “Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.”

  11. Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.”

  12. Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.”

  13. “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”

  14. Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.

  15. Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu.

  16. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai.

  17. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata.

  18. Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.

  19. Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, “I, ina zuwa da wuri.” Amin. Zo, Ubangiji Yesu!