Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Second Coming of Christ: Accompanied by Angels

4 ayoyi · 65 fannoni

Ayoyi game da Accompanied by Angels

  1. Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.

  2. “Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.

  3. Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.”

  4. yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko.