Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Roman Empire

96 ayoyi · 42 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku.

  2. Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita.

  3. Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

  4. kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.

  5. Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna.

  6. yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.

  7. Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi.

  8. ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba,

  9. ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.

  10. Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.

  11. Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.

  12. Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba.

  13. Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.

  14. Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja.

  15. Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki.

  16. Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.

  17. Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.

  18. Ubangiji yă zama tare da ruhunka. Alheri yă zama tare da ku.

  19. Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.

  20. Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.

  21. Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.