Skip to content

Barabbas

10 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Barabbas

  1. To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas.

  2. Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”

  3. Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.

  4. Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?” Suka ce, “Barabbas.”

  5. Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

  6. Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.

  7. Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.

  8. Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

  9. Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!”

  10. Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye.