Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Courts of Justice

68 ayoyi · 64 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka

  2. ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin.

  3. Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana.

  4. Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta.

  5. Kashegari, Musa ya zauna domin yă yi wa mutane shari’a, sai suka tsaya kewaye da shi daga safe har yamma.

  6. Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?”

  7. Musa ya amsa ya ce, “Saboda mutanen suna zuwa wurina, don su nemi nufin Allah.

  8. Duk lokacin da suke da gardama, akan kawo su a wurina, ni kuma sai in raba tsakaninsu, in kuma koya musu dokokin Allah da farillansa.”

  9. Surukin Musa ya amsa ya ce, “Abin da kake yi ba daidai ba ne.

  10. Kai da dukan mutanen da suke zuwa wurinka za ku gajiyar da kanku. Aikin ya fi ƙarfinka; ba za ka iya yinsa kai kaɗai ba.

  11. Ka kasa kunne gare ni yanzu, zan ba ka shawara, Allah kuma yă kasance tare da kai. Kai za ka zama wakilin mutane a gaban Allah, ka kuma kawo gardamansu gare shi.

  12. Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi.

  13. Saboda haka Musa ya fita ya gaya wa jama’a abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tattaro dattawansu saba’in, ya sa suka tsaya kewaye da Tentin Sujada.

  14. Sa’an nan Ubangiji ya sauko daga girgije, ya yi magana da shi, ya kuma ɗauke Ruhun da yake kan Musa ya ɗora shi a kan dattawa saba’in nan. Sa’ad da Ruhun ya zauna a kansu, sai suka yi annabci, amma daga wannan ba su ƙara yin haka kuma ba.

  15. To, fa, akwai dattawa biyu da suka kasance a sansani, wato, Eldad da Medad. Su ma an lasafta su cikin dattawan, amma ba su fita zuwa Tentin Sujada ba. Duk da haka Ruhun ya sauka a kansu, suka kuma yi annabci a cikin sansanin.

  16. Wani saurayi ya sheƙa a guje zuwa wajen Musa ya ce, “Eldad da Medad suna can suna annabci a sansani.”

  17. Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!”

  18. Amma Musa ya amsa ya ce, “Kana kishi domina ne? Da ma a ce dukan mutanen Ubangiji annabawa ne, da ma a kuma ce Ubangiji ya sa Ruhunsa a kansu mana!”

  19. Sai Musa da dattawan Isra’ila suka koma sansani.

  20. A wancan lokaci na faɗa muku cewa, “Ku kaya ne masu nauyi da ni kaɗai ba zan iya ɗauka ba.

  21. Ubangiji Allahnku ya ƙara yawanku har yau kuka zama da yawa kamar taurari a sarari.

  22. Bari Ubangiji, Allahn kakanninku yă ƙara yawanku sau dubu, yă kuma albarkace ku yadda ya yi alkawari!

  23. Amma yaya zan ɗauka dukan damuwoyinku da nawayarku da kuma faɗace-faɗacenku duka ni kaɗai?

  24. Ku zaɓi waɗansu masu hikima, masu ganewa, da kuma mutanen da ake girmama daga kowace kabilarku, zan kuma sa su a kanku.”

  25. Kuka amsa mini, kuka ce, “Abin da ka ce za ka yi, yana da kyau.”