Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Verdict

7 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Me kuka gani?” Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”

  2. Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”

  3. Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!”

  4. Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

  5. Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

  6. Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu.

  7. A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu.