Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Barabbas

28 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas.

  2. Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”

  3. Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi.

  4. Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”

  5. Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.

  6. Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?” Suka ce, “Barabbas.”

  7. Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!”

  8. Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”

  9. Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”

  10. Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!”

  11. Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

  12. Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.

  13. Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.

  14. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”

  15. Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.

  16. Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.

  17. Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”

  18. Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”

  19. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”

  20. Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

  21. Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!”

  22. (Barabbas yana kurkuku saboda laifin tā da hankali a birnin, da kuma don kisankai.)

  23. Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu.

  24. Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”

  25. Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.”