Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judge

91 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.

  2. Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi.

  3. Amma yaya zan ɗauka dukan damuwoyinku da nawayarku da kuma faɗace-faɗacenku duka ni kaɗai?

  4. Ku zaɓi waɗansu masu hikima, masu ganewa, da kuma mutanen da ake girmama daga kowace kabilarku, zan kuma sa su a kanku.”

  5. Kuka amsa mini, kuka ce, “Abin da ka ce za ka yi, yana da kyau.”

  6. Saboda haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu-dubu, waɗansu a kan ɗari-ɗari, waɗansu a kan hamsin-hamsin, waɗansu kuma a kan goma-goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.

  7. Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku.

  8. Kada ku nuna sonkai a cikin hukuncinku, ku saurari kowane ɓangare, babba da ƙarami, kada ku ji tsoron wani, gama hukunci na Allah ne. Ku kawo kowane batun da ya sha ƙarfinku, zan kuwa saurare shi.”

  9. Ku naɗa alƙalai da shugabanni don kowace kabila, a kowane birnin da Ubangiji Allahnku yake ba ku, za su kuma shari’anta mutane ba nuna bambanci.

  10. Kada ku ɓata shari’a, ko ku nuna bambanci. Kada ku karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta idanu mai hikima, yă murɗe maganar mai gaskiya.

  11. Gaskiya ce kaɗai za ku bi don ku rayu, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

  12. In aka kawo ƙarar da yake da wuya sosai ga alƙali a kotunanku, ko wadda aka zub da jini ne, ko ta faɗa ce, ko kuwa ta wadda aka ci mutunci ce, ku kai su wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.

  13. Ku je wurin firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, ga kuma alƙalin wanda yake mulki a lokacin. Ku bincika daga gare su, za su kuwa ba da hukunci.

  14. Dole ku aikata hukuncin da suka yi a wurin da Ubangiji zai zaɓa. Ku lura fa, ku aikata kome da suka faɗa muku.

  15. Ku yi bisa ga dokar da suka koyar muku da kuma hukuncin da suka yi muku. Kada ku juya daga abin da suka faɗa muku, ko zuwa dama, ko zuwa hagu.

  16. In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi,

  17. dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.

  18. Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne,

  19. to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  20. Idan mūsu ya tashi tsakanin mutum biyu har abin ya kai su kotu, alƙalai kuwa suka yanke hukunci a kan batun, suka kuɓutar da marar laifi sa’an nan suka hukunta mai laifi,

  21. in mai laifin ya cancanci bulala, alƙali zai sa yă kwanta a yi masa bulala a gabansa da yawan bulalan da ya dace da laifin,

  22. amma kada yă yi masa bulala fiye da arba’in. In ya yi masa fiye da haka, za a ƙasƙantar da ɗan’uwanku, zai kuma zama rainanne a idonku.

  23. To, ana nan sai waɗansu karuwai biyu suka zo wurin sarki, suka tsaya a gabansa.

  24. Sai ɗaya ta ce, “Ranka yă daɗe, wannan mata da ni muna zama a gida ɗaya. Na haifi jariri yayinda take can tare da ni.

  25. Kwana uku bayan haihuwar jaririna, wannan mata ma ta haifi jariri. Mu dai kaɗai ne; babu wani a gidan sai mu biyu.