Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judge: Priests and Levites as

8 ayoyi · 6 fannoni

Ayoyi game da Priests and Levites as

  1. Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki.

  2. “ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.

  3. Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.

  4. Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.

  5. Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.

  6. Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,

  7. suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”

  8. Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”