Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judge

91 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Da dare ɗan wannan matan ya mutu domin ta kwanta a kansa.

  2. Saboda haka ta tashi da tsakar dare ta ɗauki ɗana daga gefena yayinda baiwarka take barci. Sai ta sa shi kusa da ƙirjinta, ta kuma sa mataccen ɗanta kusa da ƙirjina.

  3. Kashegari, da na farka don in shayar da ɗana, sai na tarar ya mutu! Amma sa’ad da na dube shi da kyau da safe, sai na ga ashe ba ɗan da na haifa ba ne.”

  4. Amma ɗaya matar ta ce, “A’a! Mai rai ɗin ne ɗana; mataccen naki ne.” Amma ta farin ta nace, “A’a! Mataccen ne naki; mai ran ne nawa.” A haka suka yi ta gardama a gaban sarki.

  5. Sarki ya ce, “Wannan ta ce, ‘Ɗana ne a raye, naki ne matacce,’ yayinda ɗayan tana cewa, ‘A’a! Ɗanki ne mataccen, nawa ne a raye.’ ”

  6. Sai sarki ya ce, “Kawo mini takobi.” Sai aka kawo takobi wa sarki.

  7. Ya ba da umarni ya ce, “Yanka yaron nan mai rai, gida biyu, kowacce ta ɗauki rabi.”

  8. Ainihin mamar ɗan da yake a raye ta cika da tausayi saboda ɗanta, sai ta ce wa sarki, “Ina roƙonka, ranka yă daɗe, kada ka kashe yaron! Ka ba ta kawai!” Amma ɗayan matar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu ɗan da rai, a ci gaba a raba shi!”

  9. Sai sarki ya zartar da hukuncinsa ya ce, “A ba da jariri mai ran ga mata ta fari. Kada a kashe shi; ita ce ainihin mahaifiyarsa.”

  10. Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.

  11. To, Elisha ya riga ya ce wa matan da ya tā da ɗanta daga matattu, “Ki kwashe iyalinki ku tafi duk inda za ku tafi na ɗan lokaci, domin Ubangiji ya sa a yi yunwa na shekara bakwai a ƙasar.”

  12. Sai macen ta yi kamar yadda mutumin Allah ya faɗa. Ita da iyalinta suka tafi ƙasar Filistiyawa suka zauna shekara bakwai.

  13. A ƙarshen shekara bakwai ɗin sai ta dawo daga ƙasar Filistiyawa, ta kuma tafi wajen sarki ta roƙa a mayar mata da gidanta da filinta.

  14. Sarki kuwa yana magana da Gehazi bawan mutumin Allah, ya ce masa, “Ba ni labarin dukan abubuwan banmamakin da Elisha ya yi.”

  15. A sa’ad da Gehazi yana cikin ba shi labarin yadda Elisha ya tā da matacce ke nan, sai ga macen da aka tā da ɗanta daga matattu ta shigo don tă roƙi sarki yă mayar mata da gidanta da filinta. Gehazi ya ce, “Ranka yă daɗe, ai, ga macen, ga kuma ɗan da Elisha ya tā da daga matattu.”

  16. Sarki ya tambayi macen game da al’amarin, ita kuwa ta faɗa masa. Sa’an nan ya sa wani hafsa yă dubi damuwarta ya kuma ce masa, “Ka mayar mata kome da yake nata, haɗe da dukan kuɗin da aka samo daga filin, daga ranar da ta bar ƙasar har yă zuwa yanzu.”

  17. Ya naɗa alƙalai a kowanne daga cikin biranen katanga na Yahuda a ƙasar.

  18. Ya faɗa musu, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a.

  19. Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”

  20. A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna.

  21. Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku.

  22. Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba.

  23. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?

  24. Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci, da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya.

  25. Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.