Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Syria

235 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yayinda sarkin Isra’ila yake wucewa kusa da katanga, sai wata mace ta yi masa kuka ta ce, “Ka taimake ni, ranka yă daɗe, sarki!”

  2. Sai sarki ya amsa ya ce, “In Ubangiji bai taimake ki ba, me zan iya yi? Ina da hatsi ko ruwan inabin da zan ba ki ne?”

  3. Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Me ya faru?” Sai ta amsa ta ce, “Wannan mace ta ce mini, ‘Kawo ɗanki mu ci yau, gobe kuwa mu ci ɗana.’

  4. Saboda haka muka dafa ɗana muka ci. Kashegari na ce mata, ‘Kawo ɗanki mu ci,’ amma ta ɓoye shi.”

  5. Da yamma sai suka tashi suka tafi sansanin Arameyawa. Yayinda suka shiga tsakiyar sansanin Arameyawa kuwa, sai suka tarar ba kowa a can,

  6. gama Ubangiji ya sa rundunar Arameyawa suka ji motsin kekunan yaƙi, da motsin dawakai, da na babban rundunar sojoji, saboda haka suka ce wa juna; “Duba, sarkin Isra’ila ya ɗauka hayar sarakuna Hittiyawa da sarakunan Masarawa don su yaƙe mu!”

  7. Sai Elisha ya tafi Damaskus, Ben-Hadad mutumin Aram kuwa yana ciwo. Sa’ad da aka faɗa wa sarki, “Mutumin Allah ya hauro tun daga can zuwa nan,”

  8. Amma kashegari sai ya ɗauki tsumma mai kauri, ya jiƙa shi, ya rufe fuskar sarki da shi, har sai da sarki ya mutu. Sai Hazayel ya gāje shi a matsayin sarki.

  9. Ahaziya ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab don su yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Arameyawa suka yi wa Yoram rauni;

  10. saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni.

  11. amma Sarki Yoram ya koma Yezireyel don yă farfaɗo daga raunukan da Arameyawa suka ji masa a wata gabzawar da ya yi da Hazayel sarkin Aram.) Yehu ya ce, “In haka kuke ji, kada ku bar wani yă sulluɓe daga birnin yă kai labarin Yezireyel.”

  12. Saboda haka fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Isra’ila, kuma da daɗewa ya sa su a ƙarƙashin ikon Hazayel sarkin Aram da Ben-Hadad ɗansa.

  13. Sai Ubangiji ya tā da mai ceto wa Isra’ila, suka kuma kuɓuta daga ikon Aram. Ta haka Isra’ilawa suka yi zama a gidajensu yadda suka yi a dā.

  14. Ba abin da ya rage na rundunar Yehoyahaz sai mahayan dawakai hamsin, kekunan yaƙi goma da kuma sojoji ƙasa dubu goma. Gama sarkin Aram ya hallaka sauran, ya kuma yi kaca-kaca da su kamar ƙura a masussuka.

  15. To, Elisha ya kamu da ciwon da ya kashe shi. Yowash sarkin Isra’ila ya gangara don yă gan shi, ya kuma yi kuka dominsa. Ya yi kuka yana cewa, “Babana! Babana, keken yaƙin Isra’ila da mahayan dawakanta!”

  16. Elisha ya ce wa Yehowash, “Ka samo baka da kibiyoyi,” ya kuwa yi haka.

  17. Sai ya ce wa Yehowash sarkin Isra’ila, “Ka ɗauki baka a hannunka.” Da ya ɗauka, sai Elisha ya sa hannunsa a hannuwan sarki.

  18. Ya ce masa, “Ka buɗe taga wajen gabas,” sai ya buɗe. Sai Elisha ya ce, “Ka harba!” Sai ya harba. Elisha ya ce, “Kibiyar nasara ta Ubangiji, kibiyar nasara a kan Aram! Za ka hallaka Arameyawa sarai a Afek.”

  19. Sa’an nan ya ce, “Ka ɗauki kibiyoyi,” sai sarkin ya ɗauko. Sai Elisha ya ce, “Ka caki ƙasa.” Sai ya caka sau uku sa’an nan ya daina.

  20. Sai mutumin Allah ya yi fushi da shi ya ce, “Da a ce ka caki ƙasar sau biyar ko shida; da za ka yi nasara a kan Aram ka kuma hallaka ta sarai. Amma yanzu za ka yi nasara a kanta sau uku ne kawai.”

  21. Hazayel sarkin Aram ya musguna wa Isra’ila a duk tsawon mulkin Yehoyahaz.

  22. Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, ya kuma damu da su saboda alkawarinsa da Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Har yă zuwa yau bai yarda yă hallaka su ko yă shafe su daga gabansa ba.

  23. Hazayel sarkin Aram ya mutu, sai Ben-Hadad ɗansa ya gāje shi.

  24. Sa’an nan Yowash ya sāke ƙwato garuruwan da Ben-Hadad ya ci da yaƙi a hannun mahaifinsa Yehoyahaz. Sau uku Yehowash ya yi nasara a kansa, ta haka kuwa ya ƙwace garuruwan Isra’ilawa.

  25. Sai Rezin sarkin Aram, da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su kai wa Urushalima hari, suka kuma kewaye Ahaz, amma ba su iya shan ƙarfinsa ba.