- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Syria: Craftily drawn into a league with
Ayoyi game da Craftily drawn into a league with
Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin sarkin Isra’ila, wataƙila zai bar ka da rai.”
Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.”
Da ma abin da fadawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan’uwanka, Ben-hadad!” Sarki ya ce, “Ku je ku kawo shi.” Da Ben-Hadad ya fita, sai Ahab ya sa aka kawo shi cikin keken yaƙinsa.
Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “Bisa wannan yarjejjeniya zan sake ka.” Saboda haka ya yi yarjejjeniya da shi, sai ya bar shi ya tafi.
Ta wurin maganar Ubangiji, ɗaya daga cikin ’ya’ya maza na annabawa ya ce wa abokinsa, “Ka buge ni da makaminka,” amma mutumin ya ƙi.
Sai annabin ya ce, “Domin ba ka yi biyayya da Ubangiji ba, da zarar ka bar ni zaki zai kashe ka.” Daga baya mutumin ya tafi, zaki ya same shi, ya kuma kashe shi.
Annabin ya sami wani mutum ya ce, “Ka buge ni, ina roƙonka.” Sai mutumin ya buge shi, ya ji masa ciwo.
Sa’an nan annabin ya tafi ya tsaya a bakin hanya yana jiran sarki. Ya ɓad da kamanni da ƙyalle a kansa. Ƙyallen ya sauka zuwa bisa idanunsa.
Yayinda sarki yake wucewa, sai annabin ya yi kira da ƙarfi gare shi ya ce “Ni bawanka na tafi yaƙi, sai ga wani ya kawo mini wani mutum, ya ce, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi yă kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta, a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’
Yayinda bawanka yana fama, yana kai da kawowa, sai mutumin ya ɓace.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Hukuncinka ke nan, ka furta shi da kanka.”
Sai annabin ya cire ƙyallen da sauri daga kansa, da ya rufe idanunsa, sarkin Isra’ila kuwa ya gane shi a matsayi ɗaya daga cikin annabawa.
Sai ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka saki mutumin da na ƙudura yă mutu. Saboda haka ranka zai zama a maimakon ransa, mutanenka a maimakon mutanensa.’ ”
Cike da fushi, sarkin Isra’ila ya tafi fadarsa a Samariya.