Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sorrow

64 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can.

  2. Ki ɗaga yaron ki riƙe shi a hannu, gama zan mai da shi al’umma mai girma.”

  3. Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha.

  4. Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi.

  5. Ubangiji ya ce, “Tabbatacce na ga azabar mutanena a Masar. Na ji su suna kuka saboda matsin da shugabannin gandunsu suke musu, na kuma damu da wahalarsu.

  6. Saboda haka na sauko domin in cece su daga hannun Masarawa, in kuma fitar da su daga ƙasar Masar, in kai su ƙasa mai kyau mai fāɗi, ƙasa mai zub da madara da zuma, inda Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa suke.

  7. Yanzu kukan Isra’ilawa ya kai gare ni, na kuma ga yadda Masarawa suke wulaƙanta su

  8. To, fa, sai ka tafi. Ina aikan ka wurin Fir’auna don ka fitar da mutanena Isra’ilawa daga Masar.”

  9. Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne.

  10. Sai gaban sarki ya faɗi. Ya haura zuwa ɗakin da yake kan katangar hanyar shiga ya yi kuka. Yayinda yake tafiya ya ce, “Ya ɗana Absalom! Ɗana, ɗana Absalom! Da ma a ce ni ne na mutu maimakonka. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”

  11. Aka faɗa wa Yowab cewa, “Sarki yana kuka, yana kuma makoki saboda Absalom.”

  12. Saboda haka sai nasarar da aka yi a ranar ta zama makoki ga dukan sojoji, gama a ranar, rundunoni sun ji an ce, “Sarki yana baƙin ciki domin ɗansa.”

  13. Mutane fa suka shiga birni shiru, sai ka ce waɗanda sukan sace jiki don kunya sa’ad da suka gudo daga yaƙi.

  14. Sarki ya rufe fuskarsa ya yi kuka da ƙarfi yana cewa, “Ya ɗana Absalom! Ya Absalom ɗana, ɗana!”

  15. Sai Yowab ya shiga gidan sarki ya ce, “Yau ka kunyatar da dukan mutanenka, waɗanda ba da daɗewa ba sun ceci ranka, da rayukan ’ya’yanka maza, da na ’ya’yanka mata, da na matanka da kuma na ƙwarƙwaranka.

  16. Kana ƙaunar maƙiyinka, kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Ka bayyana a fili cewa komandodi da sojojinsu ba kome ba ne a gare ka. Na ga cewa da za ka yi farin ciki, da a ce Absalom yana da rai a yau, dukanmu kuma mun mutu.

  17. Yanzu ka fita ka ƙarfafa mutanenka. Na rantse da Ubangiji, in ba ka fita ba, babu mutum guda da za a bari tare da kai a daren nan. Wannan zai fi maka muni fiye da kowace irin masifar da ta auko maka tun ƙuruciyarka har zuwa yanzu.”

  18. Saboda haka sarki ya tashi, ya zauna a bakin hanyar shiga. Da aka faɗa wa mutane cewa, “Sarki yana zaune a bakin hanyar shiga,” sai duk suka zo gabansa. Ana cikin haka, Isra’ilawa dai sun riga sun tsere zuwa gidajensu.

  19. kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

  20. Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu.

  21. “Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa? Ku duba ku gani. Ko akwai wata wahala kamar irin wadda nake sha, wadda Ubangiji ya auko mini a cikin zafin fushinsa?

  22. Ya ɗauki Bitrus da ’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu.

  23. Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”

  24. Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”

  25. Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba?