Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Righteousness

195 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”

  2. Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”

  3. Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?”

  4. Yesu ya amsa ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”

  5. Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ”

  6. Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”

  7. Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”

  8. Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa.

  9. Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa.

  10. Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa.

  11. Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa.

  12. Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.

  13. Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’

  14. “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?”

  15. Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”

  16. Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta.

  17. Ku wawayen mutane! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ne kuma ya yi cikin ba?

  18. Ku ba matalauta abin da yake cikin kwano, kuma kome zai zama muku da tsabta.

  19. “Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.

  20. “Kaitonku, Farisiyawa, domin kun cika son wuraren zama masu daraja a majami’u, da kuma yawan gaisuwa a wuraren kasuwanci.

  21. “Kaitonku, domin ku kamar kaburbura ne da ba a sa musu alama ba, waɗanda mutane suke takawa don rashin sani.”

  22. Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.”

  23. “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa.

  24. Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa.

  25. Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’