Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Righteousness

195 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi.

  2. Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba.

  3. Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’

  4. “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne.

  5. Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ”

  6. Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki.

  7. Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.

  8. Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane ya ce,

  9. “Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji.

  10. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan.

  11. Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’

  12. “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’

  13. “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

  14. Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”

  15. Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.

  16. Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

  17. Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.”

  18. Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”

  19. Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai.

  20. Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”

  21. Sai suka hau shi da zagi suna cewa, “Kai ne dai almajirin mutumin! Mu almajiran Musa ne!

  22. Sai suka amsa suka ce, “Kai da aka haifa cike da zunubi; za ka yi karambanin koyarwar da mu!” Sai suka kore shi.

  23. Yesu ya ce, “Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.”

  24. Da Farisiyawan da suke tare da shi suka ji ya faɗi haka sai suka yi tambaya suka ce, “Mene? Mu ma makafi ne?”

  25. Yesu ya ce, “Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram.