Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Righteousness

195 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”

  2. Bayan Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku, kada ku faɗa a zuciyarku, “Ubangiji ya kawo mu a nan, mu mallaki wannan ƙasa saboda adalcinmu ne.” A’a, saboda muguntar waɗannan al’umma ne ya sa Ubangiji ya kore su a gabanku.

  3. Ba domin adalci ko mutuncinku ba ne ya sa za ku mallaki ƙasarsu; sai dai saboda muguntar al’umman nan ne ya sa Ubangiji Allahnku yana korinsu a gabanku don yă cika abin da ya rantse wa kakanninku, wato, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.

  4. Ku gane wannan, cewa ba domin adalcinku ba ne ya sa Ubangiji Allahnku yana ba ku wannan ƙasa mai kyau, ku mallaki, gama ku mutane masu taurinkai ne.

  5. Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki, amma mugaye za su lalace cikin duhu. “Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara;

  6. Da Sama’ila ya kai wurinsa, sai Shawulu ya ce, “Ubangiji yă albarkace ka, na aikata umarnin Ubangiji.”

  7. Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne, yanzu da aka kore nasara daga gare ni?

  8. Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.

  9. Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,

  10. duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.

  11. Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’

  12. Da ma Allah zai yi magana, yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba

  13. yă kuma buɗe maka asirin hikima, gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.

  14. “Ba shakka ku ne mutanen nan, hikima za tă mutu tare da ku!

  15. Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki, in kai kukana wurin Allah kai tsaye.

  16. “Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.

  17. Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa

  18. Yanzu da na shirya ƙarata, na san za a ce ba ni da laifi.

  19. Ko wani zai ce ga laifin da na yi? In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu.

  20. duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba kuma addu’ata mai tsabta ce.

  21. “Ya duniya, kada ki ɓoye jinina; bari yă yi kuka a madadina!

  22. “Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.

  23. Don me muke kamar shanu a wurinka, ka ɗauke mu mutanen wofi?

  24. Kai da ka yayyage kanka don haushi, za a yashe duniya saboda kai ne? Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?

  25. “Na san duk abin da kuke tunani, yadda za ku saɓa mini.