Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Righteousness

195 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan, tenti wurin da mugaye suke zama?’

  2. Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba? Ba ku kula da labaransu,

  3. “Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?

  4. Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?

  5. Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne.

  6. Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba.

  7. “Amma ka faɗa na ji, na ji daidai abin da ka faɗa,

  8. ‘ni mai tsarki ne marar zunubi; ina da tsabta kuma ba ni da laifi.

  9. “Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’

  10. In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku?

  11. Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai, adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai.

  12. Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara; yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi; yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni.

  13. Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni; kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.”

  14. Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara.

  15. Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.

  16. Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi.

  17. Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne, amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.

  18. Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke, amma Ubangiji yakan auna zuciya.

  19. Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa.

  20. Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa, haka ma ba shi da kyau ka nemi girma wa kanka.

  21. Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.

  22. Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba; wani dabam, ba leɓunanka ba.

  23. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu.

  24. Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

  25. Duk mai dogara ga kansa wawa ne, amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.