Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sacrifices

248 ayoyi · 55 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa.

  2. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade.

  3. Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.

  4. “ ‘Idan kuwa daga cikin ’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo ’yar tunkiya marar lahani.

  5. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta hadaya don zunubi a inda ake yankan hadayar ƙonawa.

  6. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubin da yatsarsa yă zuba a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.

  7. Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist ɗin zai yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa.

  8. Ubangiji ya ce wa Musa,

  9. “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin,

  10. ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi,

  11. sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta.

  12. Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

  13. A matsayin hakki kuwa, dole yă kawo wa firist, wato, ga Ubangiji, hadaya rago marar lahani kuma wanda aka kimanta tamaninsa daga garke don laifinsa.

  14. Ta haka firist zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.”

  15. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi na hadaya don laifi, hadaya ce tsattsarka.

  16. Za a yanka hadaya don laifi a inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, za a kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagade.

  17. Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki,

  18. da ƙodoji biyu da kitsen da yake a bisansu kusa da kwiɓi, da kuma rufin hanta, wanda za a cire tare da ƙodoji.

  19. Firist zai ƙone su a kan bagade, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Hadaya ce don laifi.

  20. Kowane da namiji cikin iyalin firistoci zai iya ci. Sai a tsattsarkan wuri ne za a ci; gama abu mafi tsarki ne.

  21. “ ‘Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ƙa’ida hanyar yinsu iri ɗaya ce. Su ɗin na firist da ya yi kafara da su ne.

  22. Tare da hadayarsa don zumunci ta godiya, zai miƙa dunƙulen burodin da aka yi da yisti.

  23. Sai wuta ta fito daga gaban Ubangiji ta cinye hadaya ta ƙonawa da sassan kitsen a kan bagaden. Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suna farin ciki, suka fāɗi rubda ciki, suka yi sujada.

  24. “Ga yadda Haruna zai shiga wuri mai tsarki, zai zo da ɗan bijimi domin hadaya don zunubi da kuma rago domin hadaya ta ƙonawa.

  25. “Sa’an nan zai yanka akuya na hadaya don zunubi saboda mutane, yă kai jinin bayan labule, yă yi da shi yadda ya yi da jinin bijimin. Zai yayyafa shi a kan murfin kafarar da kuma a gabansa.