Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Redemption

144 ayoyi · 59 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa? Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa? Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka? Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne? Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku, na mai da koguna hamada; kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa suka kuma mutu saboda ƙishi.

  2. Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace.

  3. Gama ga abin Ubangiji yana cewa, “An sayar da ke ba da kuɗi ba, kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”

  4. Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā

  5. “Zan cece ka daga hannuwan mugaye in ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.”

  6. Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.

  7. “Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba,

  8. kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

  9. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

  10. Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.

  11. Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.

  12. an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi.

  13. To, in mun mutu tare da Kiristi, mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma.

  14. An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.

  15. Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.

  16. Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.

  17. Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu.

  18. saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

  19. Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane.

  20. ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.

  21. Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu,

  22. Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.”

  23. Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,

  24. domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya.

  25. A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah