Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Redemption: Redemption money paid to priests

6 ayoyi · 59 fannoni

Ayoyi game da Redemption money paid to priests

  1. Don a fanshi ’ya’yan fari 273 na Isra’ilawa da suka fi Lawiyawa yawa,

  2. ka karɓi shekel biyar domin kowannensu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda yake da nauyin gera ashirin.

  3. Ka ba wa Haruna da ’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na ’ya’yan farin Isra’ilawa.”

  4. Haka, Musa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.

  5. Daga ’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.

  6. Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da ’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi.