Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Redemption: Is by the blood of Christ
Ayoyi game da Is by the blood of Christ
Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.
Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.
sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani.
Suka rera sabuwar waƙa, “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.