Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Redemption

144 ayoyi · 59 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta bari yă albarkaci samarin nan. Bari a kira su da sunana da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku bari kuma su ƙaru ƙwarai a bisa duniya.”

  2. “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku.

  3. “Bayan Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, ya kuma ba da ita yadda ya alkawarta muku da rantsuwa, ku da kakanninku,

  4. sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Duk ɗan farin dabbobinku na Ubangiji ne.

  5. Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. In kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Sai ku fanshe kowane ɗan farin daga cikin ’ya’yanku.

  6. “A kwanaki masu zuwa, in ɗanka ya tambaye ka, ‘Mene ne manufar wannan?’ Ka faɗa masa cewa, ‘Da hannu mai iko Ubangiji ya fito da mu daga Masar, daga ƙasar bauta.

  7. Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan ’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da ’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan ’ya’yan farina maza.’

  8. “Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su.

  9. Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji.

  10. Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji.

  11. Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku.

  12. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar.

  13. In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta,

  14. sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  15. Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  16. “ ‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi.

  17. In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba.

  18. Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna.

  19. “ ‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka.

  20. Saboda haka ana iya fansa mallakar Lawiyawa, wato, gidan da aka sayar a duk birnin da yake nasu, za a kuma mayar a Shekara ta Murna, gama gidaje a biranen Lawiyawa, mallakar Isra’ilawa ne.

  21. Amma kada a sayar da filayen kiwo na waɗannan birane; mallakarsu ce, ta ɗinɗinɗin.

  22. “ ‘In baƙo, ko wani da yake zama ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, ya wadace, ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku kuwa ya talauta, ya kuma sayar da kansa ga baƙon da yake zama a cikinku, ko memba na dangin baƙon,

  23. yana da izini samun fansa, bayan ya sayar da kansa. Ɗaya daga cikin danginsa zai iya fansarsa.

  24. Kawu ko yaron ɗan’uwan mahaifin wannan mutum, ko kuwa wani dangi a cikin zuriyarsa, zai iya fanshe shi. Ko kuma in ya azurta, zai iya fansar kansa.

  25. Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne.