Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Redemption: Is of God

5 ayoyi · 59 fannoni

Ayoyi game da Is of God

  1. To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicce ka, ya Yaƙub, shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila, “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka; na kira ka da suna; kai nawa ne.

  2. “Tuna da waɗannan abubuwa, ya Yaƙub, gama kai bawana ne, ya Isra’ila. Na yi ka, kai bawana ne; Ya Isra’ila, ba zan manta da kai ba.

  3. Na shafe laifofinka kamar girgije, zunubanka kamar hazon safe. Ka komo wurina, gama na kuɓutar da kai.”

  4. Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan; ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi. Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu, ku jeji da dukan itatuwanku, gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub, ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.

  5. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.