Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Red Sea

47 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku.

  2. “Ka ga wahalar kakanninmu a Masar; ka kuwa ji kukansu a Jan Teku.

  3. Ka aika da alamu masu banmamaki da al’ajabai a kan Fir’auna, a kan dukan shugabanninsa da kuma a kan dukan mutanen ƙasarsa, gama ka ga irin danniyar da suka yi wa mutanenka. Ka samo wa kanka suna, wadda ta dawwama har yă zuwa yau.

  4. Ka raba teku a gaban kakanninmu, saboda su wuce cikinsa a busasshiyar ƙasa, amma ka hallaka masu binsu cikin zurfafa, nutse kamar dutse a cikin ruwa.

  5. Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.

  6. Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango.

  7. Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro; amma teku ya cinye abokan gābansu.

  8. Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.

  9. Duk da haka ya cece su saboda sunansa, don yă sanar da ikonsa mai girma.

  10. Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe; ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.

  11. Ya cece su daga hannun maƙiyi; daga hannun abokin gāba ya fanshe su.

  12. Ruwaye suka rufe abokan gābansu; babu ko ɗaya da ya tsira.

  13. mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku.

  14. Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  15. Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  16. Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  17. Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya yi hanya ta cikin teku, hanya ta cikin manyan ruwaye,

  18. wanda ya ja kekunan yaƙi da dawakai, mayaƙa da kuma ƙarin mayaƙa tare ya kwantar da su a can, ba kuwa za su ƙara tashi ba, ya kashe hayaƙi daga lagwani,

  19. Ya fitar da su daga Masar ya kuma yi ayyukan da abubuwan banmamaki a Masar, a Jan Teku, da kuma cikin hamada har shekara arba’in.

  20. Ba na so ku kasance da rashin sani, ’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku.

  21. An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku.

  22. Ta wurin bangaskiya ne mutane suka bi ta cikin Jan Teku, sai ka ce a kan busasshiyar ƙasa; amma da Masarawa suka yi ƙoƙari su yi haka, sai aka nutsar da su.