Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Red Sea

47 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar.

  2. Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi.

  3. “Ka faɗa wa Isra’ilawa, su juya su kafa sansani a Fi Hahirot, a tsakanin Migdol da teku. Za su kafa sansanin kai tsaye kusa da teku, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.

  4. Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.

  5. Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan rera waƙa ga Ubangiji gama an ɗaukaka shi ƙwarai. Doki da mahayinsa ya jefa su cikin teku.

  6. Karusan Fir’auna da sojojinsa ya jefa cikin teku. Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.

  7. Wane ne cikin alloli, ya yi kamar ka, ya Ubangiji? Wane ne kamar ka, mai ɗaukaka cikin tsarki, mai banrazana cikin ɗaukaka, mai aikata al’ajabai?

  8. Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.

  9. “Zan kafa iyakokinku daga Jan Teku zuwa Bahar Rum, daga hamada kuma zuwa Kogi. Zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kuwa kore su daga gabanku.

  10. Da yake Amalekawa da Kan’aniyawa suna zama a kwarin, gobe sai ka koma baya, ka nufi wajen hamada ta hanyar Jan Teku.”

  11. Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya;

  12. Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.

  13. Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.

  14. Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.

  15. Amma ku kam, sai ku juya, ku koma cikin hamada ta hanyar Jan Teku.”

  16. Sai muka juya muka kama hanya, muka nufi hamada, ta hanyar Jan Teku yadda Ubangiji ya umarce ni. Da daɗewa muka yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun Seyir.

  17. Sai Ubangiji ya ce mini,

  18. “Kun yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun nan da daɗewa; yanzu ku juya, ku nufi arewa.

  19. ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba.

  20. Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai.

  21. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa.

  22. Lokacin da na fitar da iyayenku daga Masar, suka zo teku, sai Masarawa suka fafare su da kekunan yaƙi da dawakai har zuwa Jan Teku.

  23. Amma suka yi kuka ga Ubangiji don taimako, ya kuwa sa duhu ya raba tsakaninsu da Masarawa; ya sa teku ya rufe Masarawa. Kun gani da idanunku abin da na yi wa Masarawa, sa’an nan kuka zauna a jeji na tsawon lokaci.

  24. Amma sa’ad da suka bar Masar, Isra’ila ta bi ta hamada zuwa Jan Teku har suka zo Kadesh.

  25. Aka bayyana kwarin teku, tushen duniya suka tonu. A tsawatawar Ubangiji, da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.