Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pride

303 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai; kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai, haka na tattara dukan ƙasashe; ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki, ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ”

  2. Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma, ko zarto yă yi wa wanda yake amfani da shi taƙama? Sanda za tă girgiza mutumin da yake riƙe da ita, ko kuwa kulki yă jijjiga mutumin da yake riƙe da katako!

  3. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki, zai aukar da cuta mai kisa a kan ƙosassu jarumawa; a ƙarƙashin sansaninsa zai ƙuna wuta kamar harshen wuta.

  4. Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.

  5. Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!

  6. Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.

  7. Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.”

  8. Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami.

  9. Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido, suna tunani abin da zai same ka. “Wannan mutumin ne ya girgiza duniya ya kuma sa mulkoki suka razana,

  10. Mun ji fariyar Mowab, mun ji yawan fariyarta da girmankanta, fariyarta da reninta, amma taƙamarsu ta banza ce.

  11. Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi, za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab. Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset.

  12. Mene ne kake yi a nan kuma wa ya ba ka izini ka haƙa kabari wa kanka a nan, kana fafe kabarinka a bisa kana sassaƙa wurin hutunka a dutse?

  13. Zan tumɓuke ka daga makaminka, za a kuma kore ka daga matsayinka.

  14. Wannan ce birnin murnanku, birnin nan na tun dā wadda ƙafafunta suka kai ta zama a ƙasashe masu nesa?

  15. Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi, don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.

  16. Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane, duniya tana shan azaba ta kuma raunana, masu daraja na duniya suna shan azaba.

  17. A wannan rana Ubangiji zai hukunta ikokin da suke cikin sama da kuma sarakunan da suke a duniya.

  18. Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa ya kawar da birni mai alfarma ƙasa; ya rusa ta har ƙasa ya jefar da ita cikin ƙura.

  19. Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim, ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!

  20. Za a tattaka wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.

  21. Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada, madawwamiyar sarauniya!’ Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba.

  22. “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’

  23. Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin ’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki.

  24. Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’

  25. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa,