Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Presumption

96 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”

  2. Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji da zan yi biyayya da shi, har in bar Isra’ila su tafi? Ban san Ubangiji ba, kuma ba zan bar Isra’ila su tafi ba.”

  3. Suka ce wa Musa, “Don babu makabarta a Masar ne, ka kawo mu a hamada mu mutu? Me ka yi mana ke nan da ka fitar da mu daga Masar?

  4. Ba mu faɗa maka a Masar ba, cewa ‘Ka bar mu mu bauta wa Masarawa’? Ai, da ya fi mana mu bauta wa Masarawa, da a ce mu mutu a hamada!”

  5. Sai suka ba wa wurin suna, Massa da Meriba, saboda Isra’ilawa sun yi jayayya, suka kuma gwada Ubangiji cewa, “Ubangiji yana tsakaninmu ko babu?”

  6. Duk da haka, suka yi tsammani ba zai zama haka ba, sai suka haura ta wajen ƙasa mai tudu, Musa da akwatin alkawarin Ubangiji dai ba su gusa daga sansanin ba.

  7. “ ‘Amma duk wanda ya yi zunubi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko baƙo, ya saɓi Ubangiji, dole a ware wannan mutum daga mutanensa,

  8. tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”

  9. ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!”

  10. Kashegari dukan taron Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna suka ce, “Kun kashe mutanen Ubangiji.”

  11. suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!”

  12. Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Massa.

  13. In abin da annabin ya furta da sunan Ubangiji bai faru ba, ko bai zama gaskiya ba, saƙo ne da Ubangiji bai faɗa ba ke nan. Wannan annabi ya yi rashin hankali ne kawai. Kada ku ji tsoronsa.

  14. Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai.

  15. Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama.

  16. Amma Allah ya kashe waɗansu mutum saba’in na mutanen Bet-Shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawarin Ubangiji. Mutane kuwa suka yi makoki domin Ubangiji ya hallaka mutane da yawa.

  17. Da suka kai masussukar Nakon, sai Uzza ya miƙa hannu don yă riƙe akwatin alkawarin Allah, gama shanun sun yi tuntuɓe.

  18. Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba.

  19. Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka taka suka fita daga birnin da mayaƙa a bayansu.

  20. Sai mutumin Allah ya zo ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Domin Arameyawa suna tsammani Ubangiji allahn tuddai ne, ba allahn kwari ba, zan ba da wannan ɗumbun mayaƙa a hannuwanka, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”

  21. Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya hau ya mari Mikahiya a fuska. Ya yi tambaya, “A wace hanya ce ruhu daga Ubangiji ya bar ni ya yi maka magana?”

  22. Amma bayan Uzziya ya zama mai iko, sai ɗaga kai ya kai shi ga fāɗuwa. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa ba, ya kuma shiga haikalin Ubangiji don yă ƙone turare a bagaden turare.

  23. “Ba ku san abin da ni da kuma kakannina suka yi wa dukan mutanen sauran ƙasashe ba? Allolin ƙasashen nan sun taɓa iya ceton ƙasarsu daga hannuna ne?

  24. Wanne a cikin dukan allolin waɗannan ƙasashe da kakannina suka hallaka ya taɓa iya ceton mutanensa daga gare ni? To, yaya Allahnku zai iya cetonku daga hannuna?

  25. domin ya nuna wa Allah yatsa ya rena Allah Maɗaukaki,