Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Oppression

86 ayoyi · 8 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. kana kāre marayu da waɗanda aka danne, domin mutum, wanda yake na duniya kada ƙara haddasa wata razana.

  2. “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”

  3. daga mugaye waɗanda suke kai mini hari, daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.

  4. Me ya sa ka ɓoye fuskarka ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?

  5. Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.

  6. Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.

  7. Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.

  8. Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya; bari matalauta da mabukata su yabe sunanka.

  9. Ubangiji yana aikata adalci da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne.

  10. Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai; kada ka ni a hannun masu danne ni.

  11. Ka fanshe ni daga mutane masu danniya, don in yi biyayya da farillanka.

  12. Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu.

  13. Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.

  14. Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.

  15. Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a,

  16. Mai mulkin da ya danne talakawa yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi.

  17. waɗanda haƙoransu takuba ne waɗanda kuma muƙamuƙansu tarin wuƙaƙe ne don su cinye matalauta daga duniya da kuma mabukata daga cikin mutane.

  18. Na sāke dubawa sai na ga zaluncin da ake yi a duniya. Na ga hawayen waɗanda ake zalunta kuma ba su da mai taimako; masu iko suna goyon bayan masu zalunci, ga shi ba su da mai taimako.

  19. In ka ga ana zaluntar matalauta a wani yanki, ba a yin adalci, ana kuma tauye hakki, kada ka yi mamakin waɗannan abubuwa; domin akwai wani jami’in da yake bisa da wani, a bisansu biyu kuwa akwai wani.

  20. Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa, cin hanci kuma yakan lalace hali.

  21. Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci. Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta. Ku ba wa marayu hakkinsu, ku taimaki gwauruwa.

  22. Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje kuke kuma haɗa gonaki da gonaki har babu sauran filin da ya rage ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar.

  23. Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,

  24. shi ne mutumin da zai zauna a bisa, wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse. Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.

  25. Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe, na yi kuka kamar kurciya mai makoki. Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai. Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”