Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles

338 ayoyi · 37 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce.

  2. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu,

  3. don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”

  4. Fadawan Fir’auna suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai zama mana tarko? Ka bar mutanen su tafi domin su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Har yanzu ba ka san cewa Masar ta lalace ba?”

  5. Fir’auna ya kira Musa da Haruna da gaggawa ya ce, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

  6. Yanzu ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yă ɗauke wannan muguwar annoba daga gare ni.”

  7. To, fa, sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya.

  8. Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila.

  9. Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.

  10. Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna zai ƙi kasa kunne gare ka, sai na ƙara aikata waɗansu mu’ujizai cikin Masar.”

  11. Da tsakar dare, sai Ubangiji ya karkashe dukan ’ya’yan fari a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato, magājinsa, har zuwa ɗan fari na ɗan sarƙa da yake kurkuku, har da ’ya’yan fari na dabbobi.

  12. Fir’auna da dukan fadawansa da kuma dukan Masarawa, suka tashi a cikin daren da kuka mai zafi, aka kuma ji kukan a ko’ina a cikin ƙasar Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.

  13. A cikin daren, Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tashi, ku da jama’arku, ku fita daga cikin jama’ata. Ku tafi, ku bauta wa Ubangiji yadda kuka ce.

  14. Ku kwashi garkunanku na tumaki da na awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.”

  15. Masarawa suka matsa wa Isra’ilawa su fita daga ƙasarsu da sauri. Gama mutanen Masar sun ce, “Ai, za mu mutu duka, in ba su tafi ba!”

  16. Zan kuma taurare zuciyar Fir’auna, zai kuwa bi su. Na shirya wannan domin in nuna ɗaukakata a bisa Fir’auna da ƙungiyar sojansa. Bayan wannan, mutanen Masar za su sani ni ne Ubangiji.” Sai Isra’ilawa suka yi haka.

  17. Masarawa za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na sami nasara bisa kan Fir’auna, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa.”

  18. Da asubahin fāri, sai Ubangiji ya dubi ƙasa a kan sojojin Masarawa daga al’amudin wuta da kuma girgije, sai ya sa suka ruɗe.

  19. Ya sa ƙafafun keken yaƙinsu suka fita don su kāsa tuƙi. Sai Masarawa suka ce, “Bari mu gudu daga Isra’ilawa gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masar.”

  20. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga iko mai girma da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa, sai mutanen suka ji tsoron Ubangiji, suka amince da shi, da kuma bawansa Musa.

  21. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan zubo muku burodi kamar ruwa daga sama. Mutanen za su fita kowace rana su tattara abin da zai ishe su na ranan. Ta haka zan gwada su in ga ko za su bi umarnaina.

  22. A rana ta shida za su shirya abin da suka kwaso, wannan kuwa zai zama ninki biyu na abin da sukan tattara na sauran ranaku.”

  23. Saboda haka Musa da Haruna suka ce wa dukan Isra’ila, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fitar da ku daga Masar.

  24. ‘Ku da kanku kun ga abin da na yi wa Masar, da yadda na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa na kawo ku wurina.

  25. Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce,