Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles

338 ayoyi · 37 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!”

  2. Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”

  3. Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.

  4. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.

  5. Saboda haka manyan firistoci suka ƙulla su kashe Lazarus shi ma,

  6. gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi.

  7. Mutane da yawa kuwa suka fita taryensa, saboda sun ji labarin abin banmamakin da ya yi.

  8. Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba.

  9. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba.

  10. Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana.

  11. Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba.

  12. An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.

  13. “Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.

  14. Wata rana, Bitrus da Yohanna suna haurawa zuwa haikali a lokacin addu’a da ƙarfe uku na rana.

  15. To, sai ga wani da aka haifa gurgu ana ɗauke da shi zuwa ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, inda akan ajiye kowace rana, don yă yi bara daga masu shigowa cikin filayen haikali.

  16. Da ya ga Bitrus da Yohanna suna gab da shiga, sai ya roƙe su kuɗi.

  17. Bitrus kuwa ya kafa masa ido, haka ma Yohanna. Sai Bitrus ya ce, “Dube mu!”

  18. Saboda haka mutumin ya mai da hankalinsa a kansu, yana fata samun wani abu daga gare su.

  19. Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.”

  20. Ta wurin kama hannunsa na dama, ya taimake shi ya miƙe, nan take ƙafafu da idon sawun mutumin suka yi ƙarfi.

  21. Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah.

  22. Sa’ad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah,

  23. sai suka gane cewa shi ne mutumin nan wanda dā yake zama yana bara a bakin ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, suka kuwa cika da mamaki da tsoro a kan abin da ya faru gare shi.

  24. Da Bitrus ya ga haka, sai ya ce musu, “Mutanen Isra’ila, don me wannan ya ba ku mamaki? Don me kuke kallonmu sai ka ce da ikon kanmu ne ko kuwa don ibadarmu ne muka sa wannan mutum ya yi tafiya?

  25. Ta wurin bangaskiya cikin sunan Yesu ne wannan mutum da kuke gani kuka kuma sani ya sami ƙarfi. Da sunan Yesu, da kuma bangaskiyar da take samuwa ta wurinsa ne ya ba shi cikakkiyar warkarwa, yadda dukanku kuke gani.