Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert

759 ayoyi · 177 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.

  2. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.

  3. Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki.

  4. Kwana shida za ka yi dukan aikinka,

  5. amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.

  6. Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  7. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  8. Ba za ka yi kisankai ba.

  9. Ba za ka yi zina ba.

  10. Ba za ka yi sata ba.

  11. Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

  12. Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”

  13. Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa

  14. suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.”

  15. Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”

  16. Sa’ad da mutane suka tsattsaya da nesa, sai Musa ya matsa kusa da girgije mai duhu, inda Allah yake.

  17. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa wannan. ‘Kun gani da kanku cewa na yi magana da ku daga sama.

  18. Kada ku yi waɗansu alloli in ban da ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa ko na zinariya.

  19. “ ‘Ku yi mini bagaden ƙasa, ku kuma miƙa mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, za ku hadayar da tumakinku da awakinku da shanu. Duk inda na sa a girmama sunana, zan zo wurinku, in sa muku albarka.

  20. In kuka yi mini bagade dutse, kada ku gina shi da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama inda guduma ta taɓa duwatsun, sun haramtu ke nan.

  21. Kada ku gina wa bagadena matakala, domin kada yayinda wani yana hawa, mutane su ga tsiraicinsa.’

  22. Sa’ad da Musa ya tafi ya faɗa wa mutanen duk kalmomin Ubangiji da dokokinsa, sai suka amsa da murya ɗaya suna cewa, “Duk abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi.”

  23. Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila.

  24. Sai ya aiki samarin Isra’ilawa, suka miƙa hadaya ta ƙonawa, suka kuma miƙa ƙananan bijimai don hadaya ta salama ga Ubangiji.

  25. Musa ya ɗauki rabin jinin ya zuba a cikin kwanoni, rabin kuma ya yayyafa a kan bagaden.