Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba, Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba.

  2. Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya? Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya?

  3. In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,

  4. ’yan adam duka za su hallaka tare, mutum kuma zai koma ƙasa.

  5. “In kana da ganewa sai ka saurari wannan; ka saurari abin da zan ce.

  6. Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?

  7. Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’ ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’

  8. wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.

  9. Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare; an girgiza mutanen amma sun wuce; an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba.

  10. “Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka.

  11. Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu, inda masu aikata mugunta za su ɓoye.

  12. Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane, har da za su zo gabansa don yă shari’anta su.

  13. Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko, yă kuma sa waɗansu a wurinsu.

  14. Gama yana sane da abubuwan da suke yi, yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su.

  15. Yana ba su horo, don muguntarsu, inda kowa zai gan su,

  16. domin sun juya daga binsa, kuma ba su kula da hanyoyinsa ba.

  17. Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa yadda ya kai ga jin kukan masu bukata.

  18. Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,

  19. yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki, ya hana shi sa wa mutane tarko.

  20. “Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle.

  21. Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa, tsawar da take fita daga bakinsa.

  22. Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.

  23. Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo; Ya tsawata da muryarsa mai girma. Sa’ad da ya sāke yin tsawa ba ya rage wani abu.

  24. Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi; yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.

  25. Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’