Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Adoption

129 ayoyi · 38 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya.

  2. Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.”

  3. Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.

  4. A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri.

  5. Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.

  6. A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi.

  7. Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma.

  8. Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Al’ummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Isra’ila, sun zama gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.

  9. wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna.

  10. Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya,

  11. don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya

  12. Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”?

  13. Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.

  14. Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa.

  15. Ya ce, “Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana; a gaban jama’a zan rera yabonka.”

  16. Har wa yau ya ce, “Zan dogara gare shi.” Ya kuma ce, “Ga ni, da ’ya’yan da Allah ya ba ni.”

  17. Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

  18. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”

  19. Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?

  20. In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba.

  21. Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba!

  22. Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa.

  23. Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

  24. Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.

  25. Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.