Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Adoption: Subjects saints to the fatherly discipline of God

11 ayoyi · 38 fannoni

Ayoyi game da Subjects saints to the fatherly discipline of God

  1. Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku.

  2. Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata.

  3. Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,

  4. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.

  5. Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

  6. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”

  7. Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?

  8. In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba.

  9. Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba!

  10. Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa.

  11. Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.