Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Adoption: Of Gentiles, predicted

5 ayoyi · 38 fannoni

Ayoyi game da Of Gentiles, predicted

  1. Zan dasa ta wa kaina a ƙasar; zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’ Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba,’ ‘Ku mutanena ne’; za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’ ”

  2. har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai?

  3. Kamar yadda ya faɗa a Hosiya. “Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba; zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”

  4. kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ”

  5. Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Al’ummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Isra’ila, sun zama gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.