Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Adoption: Is of God's grace

9 ayoyi · 38 fannoni

Ayoyi game da Is of God's grace

  1. ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Urushalima, Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne; mahaifinki mutumin Amoriyawa ne, mahaifiyarki kuma mutuniyar Hitti ce.

  2. A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki.

  3. Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki.

  4. “ ‘Sa’an nan na wuce na ga kina birgima cikin jininki, yayinda kike kwance can cikin jininki sai na ce miki, “Ki rayu!”

  5. Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka.

  6. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.

  7. A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri.

  8. Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.

  9. A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi.