Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Adoption: Should lead to holiness

6 ayoyi · 38 fannoni

Ayoyi game da Should lead to holiness

  1. Saboda haka, “Sai ku fito daga cikinsu, ku keɓe kanku, in ji Ubangiji. Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, zan kuma karɓe ku.”

  2. Kuma, “Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama ’ya’yana, maza da mata, in ji Ubangiji Maɗaukaki.”

  3. Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.

  4. don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya

  5. Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.

  6. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.