- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 5:2kusan 1451 K.H.
Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb.
- Maimaitawar Shari’a 5:3kusan 1451 K.H.
Ba da kakanninmu ba ne Ubangiji ya yi wannan alkawari, amma da mu ne, da dukanmu waɗanda muke da rai a yau.
- Maimaitawar Shari’a 5:4kusan 1451 K.H.
Ubangiji ya yi magana fuska da fuska da ku daga wuta a kan dutse.
- Maimaitawar Shari’a 5:5kusan 1451 K.H.
(A wannan lokaci na tsaya tsakanin Ubangiji da ku, don in furta muku maganar Ubangiji, domin kun ji tsoron wutar, ba ku kuwa hau dutsen ba.) Ya ce,
- Maimaitawar Shari’a 5:6kusan 1451 K.H.
“Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.
- Maimaitawar Shari’a 5:7kusan 1451 K.H.
“Ba za ka kasance da waɗansu alloli a gabana ba.
- Maimaitawar Shari’a 5:8kusan 1451 K.H.
Ba za ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da take a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa ba.
- Maimaitawar Shari’a 5:9kusan 1451 K.H.
Ba za ka rusuna musu, ko ka yi musu sujada ba. Gama Ni, Ubangiji Allahnka, Allah ne mai kishi, nakan hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyaye har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni.
- Maimaitawar Shari’a 5:10kusan 1451 K.H.
Amma nakan nuna ƙauna ga dubban tsararraki na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye dokokina.
- Maimaitawar Shari’a 5:11kusan 1451 K.H.
Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai ba wa duk mai yin amfani da sunansa a banza laifi.
- Maimaitawar Shari’a 5:12kusan 1451 K.H.
Ka kiyaye ranar Asabbaci ta wurin kiyaye ta da tsarki, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka.
- Maimaitawar Shari’a 5:13kusan 1451 K.H.
Kwanaki shida za ka yi aiki, ka kuma yi dukan aikinka,
- Maimaitawar Shari’a 5:14kusan 1451 K.H.
amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka.
- Maimaitawar Shari’a 5:15kusan 1451 K.H.
Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar amma Ubangiji Allahnka ya fitar da kai daga can da iko da kuma ƙarfi. Saboda haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabbaci.
- Maimaitawar Shari’a 5:16kusan 1451 K.H.
Ka ba da girma ga mahaifinka da mahaifiyarka, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka, don ka yi tsawon rai, ka kuma sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
- Maimaitawar Shari’a 5:17kusan 1451 K.H.
Kada ka yi kisankai.
- Maimaitawar Shari’a 5:18kusan 1451 K.H.
Kada ka yi zina.
- Maimaitawar Shari’a 5:19kusan 1451 K.H.
Kada ka yi sata.
- Maimaitawar Shari’a 5:20kusan 1451 K.H.
Kada ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka.
- Maimaitawar Shari’a 5:21kusan 1451 K.H.
Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi sha’awar gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko bayinsa maza da mata, ko saniyarka, ko jakinsa, ko dai wani abin da yake na maƙwabtanka.”
- Maimaitawar Shari’a 5:22kusan 1451 K.H.
Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya furta da babbar murya ga taronku gaba ɗaya, a can dutse ta tsakiyar wuta, girgije da kuma baƙin duhu; bai kuma ƙara kome ba. Sa’an nan ya rubuta su a kan alluna biyu na dutse, ya kuma ba ni su.
- Maimaitawar Shari’a 5:23kusan 1451 K.H.
Sa’ad da kuka ji muryar daga duhu, yayinda dutsen yana cin wuta, dukan manyan kabilanku da dattawanku suka zo wurina.
- Maimaitawar Shari’a 5:24kusan 1451 K.H.
Kuka kuma ce, “Ubangiji Allahnmu ya nuna mana ɗaukakarsa da zatinsa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. A yau mun ga cewa mutum zai iya rayu idan ma Allah ya yi magana da shi.
- Maimaitawar Shari’a 5:25kusan 1451 K.H.
Amma yanzu, don me za mu mutu? Wannan wuta mai girma za tă cinye mu, za mu kuwa mutu in muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu.
- Maimaitawar Shari’a 5:26kusan 1451 K.H.
Gama wanda ɗan adam ne ya taɓa jin muryar Allah mai rai yana magana daga wuta, kamar yadda muka ji, ya kuma tsira?