Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 34:14kusan 1452 K.H.

    saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu.

  2. Ƙidaya 34:15kusan 1452 K.H.

    Waɗannan kabilu biyu da rabi, sun sami gādonsu a wancan hayin Urdun a gabashin Yeriko wajen fitowar rana.”

  3. Ƙidaya 34:16kusan 1452 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  4. Ƙidaya 34:17kusan 1452 K.H.

    “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.

  5. Ƙidaya 34:18kusan 1452 K.H.

    Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.

  6. Ƙidaya 34:19kusan 1452 K.H.

    “Ga sunayensu. “Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;

  7. Ƙidaya 34:20kusan 1452 K.H.

    Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon

  8. Ƙidaya 34:21kusan 1452 K.H.

    Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;

  9. Ƙidaya 34:22kusan 1452 K.H.

    Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;

  10. Ƙidaya 34:23kusan 1452 K.H.

    Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;

  11. Ƙidaya 34:24kusan 1452 K.H.

    Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;

  12. Ƙidaya 34:25kusan 1452 K.H.

    Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;

  13. Ƙidaya 34:26kusan 1452 K.H.

    Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;

  14. Ƙidaya 34:27kusan 1452 K.H.

    Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;

  15. Ƙidaya 34:28kusan 1452 K.H.

    Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”

  16. Ƙidaya 34:29kusan 1452 K.H.

    Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.

  17. Ƙidaya 35:1kusan 1451 K.H.

    A filayen Mowab, wajen Urdun, ɗaura da Yeriko, Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,

  18. Ƙidaya 35:2kusan 1451 K.H.

    “Ka umarci Isra’ilawa su ba wa Lawiyawa garuruwan da za su zauna a ciki daga cikin gādon da Isra’ilawa za su mallaka. A kuma ba su wurin kiwo kewaye da garuruwan.

  19. Ƙidaya 35:3kusan 1451 K.H.

    Sa’an nan za su kasance da garuruwan da za su zauna, su sami fili, da kuma za su yi kiwon garkensu na shanu da tumaki da kuma sauran dabbobinsu.

  20. Ƙidaya 35:4kusan 1451 K.H.

    “Wuraren kiwo a kewayen garuruwan da za a ba wa Lawiyawa, girmansu zai zama mai fāɗin kamu dubu ɗaya daga katangar garin.

  21. Ƙidaya 35:5kusan 1451 K.H.

    A bayan garin, ka auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu wajen kudu, da kuma kamu dubu uku wajen arewa, a bar garin a tsakiya. Za su kasance da wannan a matsayin wurin kiwo na garuruwan.

  22. Ƙidaya 35:6kusan 1451 K.H.

    “A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida daga cikin garuruwan za su zama biranen mafaka, inda wanda ya kashe mutum zai gudu yă je. Ban da wannan, a ba su waɗansu garuruwa arba’in da biyu.

  23. Ƙidaya 35:7kusan 1451 K.H.

    Duka-duka dai a ba Lawiyawa garuruwa arba’in da takwas, tare da wuraren kiwonsu.

  24. Ƙidaya 35:8kusan 1451 K.H.

    Garuruwan da za ku ba wa Lawiyawa daga ƙasar da Isra’ilawa suka mallaka, za a ba da su bisa girman gādon kowace kabila. Ka karɓi garuruwa masu yawa daga kabilar da take da garuruwa masu yawa, amma kaɗan daga kabilar da ba ta da garuruwa masu yawa.”

  25. Ƙidaya 35:9kusan 1451 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,