- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 35:10kusan 1451 K.H.
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana,
- Ƙidaya 35:11kusan 1451 K.H.
ku zaɓi waɗansu garuruwan da za su zama biranen mafakarku, inda wanda ya kashe mutum cikin kuskure zai iya gudu zuwa.
- Ƙidaya 35:12kusan 1451 K.H.
Za su zama wuraren mafaka daga hannun mai bin hakki, don kada a kashe mai kisankai, tun ba a kai shi gaban shari’a, a gaban taron jama’a ba.
- Ƙidaya 35:13kusan 1451 K.H.
Waɗannan garuruwa shida da aka bayar za su zama biranen mafakarku.
- Ƙidaya 35:14kusan 1451 K.H.
A ba da uku a wannan gefe na Urdun, a kuma ba da uku a Kan’ana, su zama biranen mafaka.
- Ƙidaya 35:15kusan 1451 K.H.
Waɗannan garuruwa shida za su zama wurin mafaka wa Isra’ilawa, baƙi da duk sauran mutanen da suke zama a cikinsu, saboda duk wanda ya kashe mutum cikin kuskure yă iya gudu zuwa.
- Ƙidaya 35:16kusan 1451 K.H.
“ ‘In wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, to, shi mai kisankai ne; sai a kashe mai kisankan nan.
- Ƙidaya 35:17kusan 1451 K.H.
Ko kuwa in wani yana riƙe da dutsen da ya isa yă kashe mutum a hannunsa, ya kuma harbi wani da dutsen har ya mutu, to, shi mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan.
- Ƙidaya 35:18kusan 1451 K.H.
Ko kuwa wani yana da makami na itace a hannunsa da ya isa yă kashe mutum, ya kuma bugi wani da shi har ya mutu, shi ma mai kisankai ne, sai a kashe mai kisankan nan.
- Ƙidaya 35:19kusan 1451 K.H.
Sai mai bin hakkin jinin yă kashe mai kisankan, sa’ad da ya sadu da mai kisankan, sai yă kashe shi.
- Ƙidaya 35:20kusan 1451 K.H.
In saboda ƙiyayya, mutum ya laɓe, ya soke wani, ko ya jefe shi da wani abu da gangan har ya mutu,
- Ƙidaya 35:21kusan 1451 K.H.
ko kuwa saboda ƙiyayya ya naushe shi har ya mutu, sai a kashe wannan mutumin da ya yi haka; shi mai kisankai ne. Sai mai bin hakkin jini yă kashe mai kisankan in ya same shi.
- Ƙidaya 35:22kusan 1451 K.H.
“ ‘Amma in cikin tsautsayi ne ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuma ya jefe shi, ba da gangan ba,
- Ƙidaya 35:23kusan 1451 K.H.
ko kuwa bai gan shi ba, ya jefa dutsen da zai kashe shi a kansa, ya kuwa mutu, to, da yake shi ba abokin gābansa ba ne, bai kuma yi nufi yă ji masa ba,
- Ƙidaya 35:24kusan 1451 K.H.
dole taro su yi hukunci tsakanin mai laifin, da mai bin hakkin jini bisa waɗannan ƙa’idodi.
- Ƙidaya 35:25kusan 1451 K.H.
Dole taro su kāre wanda ake zargi da kisa, daga mai bin hakkin jini. Su mai da shi birnin mafaka inda ya gudu ya tafi. Dole yă kasance a can sai mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai tsarki.
- Ƙidaya 35:26kusan 1451 K.H.
“ ‘Amma in wanda ake zargin ya kuskura ya fita, ya kai iyakar birnin mafaka wadda ya gudu ya je,
- Ƙidaya 35:27kusan 1451 K.H.
idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan gari, mai bin hakkin jinin zai iya kashe mai kisankai ɗin ba tare da wani laifi ba.
- Ƙidaya 35:28kusan 1451 K.H.
Dole wanda ake zargin, yă kasance a birninsa na mafaka sai bayan mutuwa babban firist; sai bayan mutuwar babban firist ne kawai zai iya komo ga mallakarsa.
- Ƙidaya 35:29kusan 1451 K.H.
“ ‘Waɗannan su ne za su zama ƙa’idodin da za ku kasance da su, a dukan tsararraki masu zuwa.
- Ƙidaya 35:30kusan 1451 K.H.
“ ‘Kowa da ya kashe wani, za a kashe shi a matsayin mai kisankai, bisa ga shaidar shaidu. Amma kada a kashe wani bisa ga shaidar mutum ɗaya.
- Ƙidaya 35:31kusan 1451 K.H.
“ ‘Kada a karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, wanda ya cancanci mutuwa. Lalle ne a kashe shi.
- Ƙidaya 35:32kusan 1451 K.H.
“ ‘Kada a karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don yă koma yă zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba.
- Ƙidaya 35:33kusan 1451 K.H.
“ ‘Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama a ciki. Zub da jini yakan ƙazantar da ƙasa, ba a kuma iya yin kafara saboda wannan ƙasa da aka zub da jini, sai dai ta wurin jinin mutumin da ya zub da jinin.
- Ƙidaya 35:34kusan 1451 K.H.
Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama, wadda ni kuma nake zama a ciki, gama Ni Ubangiji, ina zama a cikin Isra’ilawa.’ ”