Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Markus 13:3kusan 33 M.

    Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce,

  2. Markus 13:4kusan 33 M.

    “Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?”

  3. Markus 13:5kusan 33 M.

    Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku.

  4. Markus 13:6kusan 33 M.

    Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa.

  5. Markus 13:7kusan 33 M.

    Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna.

  6. Markus 13:8kusan 33 M.

    Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.

  7. Markus 13:9kusan 33 M.

    “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.

  8. Markus 13:10kusan 33 M.

    Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.

  9. Markus 13:11kusan 33 M.

    Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.

  10. Markus 13:12kusan 33 M.

    “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.

  11. Markus 13:13kusan 33 M.

    Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

  12. Markus 13:14kusan 33 M.

    “Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’tsaye indabai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.

  13. Markus 13:15kusan 33 M.

    Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu.

  14. Markus 13:16kusan 33 M.

    Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa.

  15. Markus 13:17kusan 33 M.

    Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!

  16. Markus 13:18kusan 33 M.

    Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi.

  17. Markus 13:19kusan 33 M.

    Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.

  18. Markus 13:20kusan 33 M.

    “Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin.

  19. Markus 13:21kusan 33 M.

    A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata.

  20. Markus 13:22kusan 33 M.

    Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.

  21. Markus 13:23kusan 33 M.

    Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.

  22. Markus 13:24kusan 33 M.

    “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan, “ ‘rana za tă yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba;

  23. Markus 13:25kusan 33 M.

    taurari za su fāffāɗo daga sararin sama. Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’

  24. Markus 13:26kusan 33 M.

    “Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma.

  25. Markus 13:27kusan 33 M.

    Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama.