circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Luka 21:19kusan 33 M.
Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.
- Luka 21:20kusan 33 M.
“In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa.
- Luka 21:21kusan 33 M.
A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin.
- Luka 21:22kusan 33 M.
Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta.
- Luka 21:23kusan 33 M.
Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan.
- Luka 21:24kusan 33 M.
Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ’yan kurkuku, zuwa dukan al’ummai. Al’ummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Al’ummai ya cika.
- Luka 21:25kusan 33 M.
“Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.
- Luka 21:26kusan 33 M.
Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama.
- Luka 21:27kusan 33 M.
A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma.
- Luka 21:28kusan 33 M.
Sa’ad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”
- Luka 21:29kusan 33 M.
Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa.
- Luka 21:30kusan 33 M.
A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa.
- Luka 21:31kusan 33 M.
Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.
- Luka 21:32kusan 33 M.
“Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika.
- Luka 21:33kusan 33 M.
Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
- Luka 21:34kusan 33 M.
“Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.
- Luka 21:35kusan 33 M.
Gama za tă zo a kan kowa da yake kan dukan duniya.
- Luka 21:36kusan 33 M.
Ku yi tsaro kullum, ku yi addu’a don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.”
- Luka 21:37kusan 33 M.
Kowace rana, Yesu yakan je haikalin ya yi koyarwa, da kowace yamma kuma, ya je ya kwana a kan tudun da ake kira Dutsen Zaitun.
- Luka 21:38kusan 33 M.
Da sassafe kuma, dukan mutanen suka zo haikalin, don su saurare shi.
- Luka 22:1kusan 33 M.
Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa,
- Luka 22:2kusan 33 M.
manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane.
- Luka 22:3kusan 33 M.
Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun.
- Luka 22:4kusan 33 M.
Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su.
- Luka 22:5kusan 33 M.
Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi.