circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Luka 20:41kusan 33 M.
Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’
- Luka 20:42kusan 33 M.
Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,
- Luka 20:43kusan 33 M.
sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’
- Luka 20:44kusan 33 M.
Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”
- Luka 20:45kusan 33 M.
Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa,
- Luka 20:46kusan 33 M.
“Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa.
- Luka 20:47kusan 33 M.
Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen addu’o’i. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.”
- Luka 21:1kusan 33 M.
Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a ma’ajin haikalin.
- Luka 21:2kusan 33 M.
Ya kuma ga wata gwauruwa matalauciya, ta saka anini biyu.
- Luka 21:3kusan 33 M.
Sai ya ce, “Gaskiya ina faɗa muku, wacce nan gwauruwa matalauciya ta sa fiye da dukan sauran.
- Luka 21:4kusan 33 M.
Dukan mutanen nan sun ba da baikonsu daga cikin arzikinsu ne, amma ita daga cikin talaucinta, ta saka duk abin da take da shi na rayuwa.”
- Luka 21:5kusan 33 M.
Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce,
- Luka 21:6kusan 33 M.
“Wannan abin da kuke kallo a nan, lokaci yana zuwa da ba za a bar wani dutse a kan wani dutse ba. Kowannensu, za a rushe shi.”
- Luka 21:7kusan 33 M.
Suka tambaye shi suka ce, “Malam, yaushe waɗannan za su faru? Kuma wace alama za tă nuna cewa suna dab da faruwa?”
- Luka 21:8kusan 33 M.
Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su.
- Luka 21:9kusan 33 M.
Sa’ad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”
- Luka 21:10kusan 33 M.
Sai ya ce musu, “Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki zai tasar wa mulki.
- Luka 21:11kusan 33 M.
Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.
- Luka 21:12kusan 33 M.
“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.
- Luka 21:13kusan 33 M.
Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.
- Luka 21:14kusan 33 M.
Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku.
- Luka 21:15kusan 33 M.
Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.
- Luka 21:16kusan 33 M.
Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.
- Luka 21:17kusan 33 M.
Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.
- Luka 21:18kusan 33 M.
Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba.