- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Zakariya 13:5kusan 487 K.H.
Zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne. Ni manomi ne; ƙasa ce nake samun abin zaman gari tun ina matashi.’
- Zakariya 13:6kusan 487 K.H.
In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’
- Zakariya 13:7kusan 487 K.H.
“Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina, mutumin da yake kusa da ni sosai!” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kashe makiyayin, sai tumakin su watse, in kuma tayar wa ƙananan.
- Zakariya 13:8kusan 487 K.H.
A cikin ƙasar duka,” in ji Ubangiji, “kashi biyu bisa uku za a buge su su hallaka; duk da haka za a bar kashi ɗaya bisa uku a cikinta.
- Zakariya 13:9kusan 487 K.H.
Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’ ”
- Zakariya 14:1kusan 487 K.H.
Ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba muku ganimar da aka washe daga gare ku.
- Zakariya 14:2kusan 487 K.H.
Zan tara dukan al’ummai su yaƙi Urushalima; za a ci birnin da yaƙi, za a washe gidaje, a kuma yi wa mata fyaɗe. Rabin birnin zai je bauta, amma ba za a kwashe sauran mutanen daga birnin ba.
- Zakariya 14:3kusan 487 K.H.
Sa’an nan Ubangiji zai fita yă yi yaƙi da waɗannan al’ummai, kamar yadda yake yaƙi a ranar yaƙi.
- Zakariya 14:4kusan 487 K.H.
A ranan nan ƙafafunsa za su tsaya a kan Dutsen Zaitun, gabas da Urushalima, za a kuma tsage Dutsen Zaitun kashi biyu daga gabas zuwa yamma, yă zama babban kwari, rabin dutsen zai matsa zuwa wajen arewa, rabi kuma zai matsa zuwa wajen kudu.
- Zakariya 14:5kusan 487 K.H.
Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki.
- Zakariya 14:6kusan 487 K.H.
A ranan nan ba za a kasance da haske ko sanyi ba, ko hazo mai duhu ba.
- Zakariya 14:7kusan 487 K.H.
Za tă zama rana ce ta musamman, ba yini ko dare, rana da take sananne ga Ubangiji. Sa’ad da yamma ta yi, za a yi haske.
- Zakariya 14:8kusan 487 K.H.
A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum, a damina da rani.
- Zakariya 14:9kusan 487 K.H.
Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa.
- Zakariya 14:10kusan 487 K.H.
Ƙasar gaba ɗaya daga Geba zuwa Rimmon, kudu da Urushalima, za tă zama kamar Araba. Amma Urushalima za tă kasance a wurinta, daga Ƙofar Benyamin zuwa sashen Ƙofa ta Farko, zuwa Ƙofar Kusurwa, daga kuma Hasumiyar Hananel zuwa wurin matsin ruwan inabin sarki.
- Zakariya 14:11kusan 487 K.H.
Za a zauna a cikinka; ba za a ƙara hallaka ta ba. Urushalima za tă zauna lafiya.
- Zakariya 14:12kusan 487 K.H.
Ga bala’in da Ubangiji zai bugi dukan al’umman da suka yi yaƙi da Urushalima. Fatar jikinsu za tă ruɓe tun suna tsaye a ƙafafunsu, idanunsu za su ruɓe a cikin kwarminsu, harsunansu kuma zai ruɓe a cikin bakunansu.
- Zakariya 14:13kusan 487 K.H.
A ranan nan Ubangiji zai sa maza su cika da tsoro ƙwarai. Kowane mutum zai kama hannun ɗan’uwansa, za su kai wa juna hari.
- Zakariya 14:14kusan 487 K.H.
Yahuda ma za tă yi yaƙi a Urushalima. Za a tattara dukiyar al’umman da suke kewaye, za a tara zinariya da azurfa masu yawan gaske tare da tufafi.
- Zakariya 14:15kusan 487 K.H.
Irin wannan bala’i zai auko wa dawakai da alfadarai, raƙuma da jakuna, da kuma dukan dabbobi a wannan sansani.
- Zakariya 14:16kusan 487 K.H.
Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul.
- Zakariya 14:17kusan 487 K.H.
In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba.
- Zakariya 14:18kusan 487 K.H.
In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.
- Zakariya 14:19kusan 487 K.H.
Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.
- Zakariya 14:20kusan 487 K.H.
A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade.