Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Malaki 2:11kusan 397 K.H.

    Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah.

  2. Malaki 2:12kusan 397 K.H.

    Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki.

  3. Malaki 2:13kusan 397 K.H.

    Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki.

  4. Malaki 2:14kusan 397 K.H.

    Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.

  5. Malaki 2:15kusan 397 K.H.

    Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.

  6. Malaki 2:16kusan 397 K.H.

    “Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana.

  7. Malaki 2:17kusan 397 K.H.

    Kun sa Ubangiji Maɗaukaki ya gaji da maganganunku. Sai kuka ce, “Yaya muka sa ya gaji?” Kun yi haka ta wurin cewa, “Duk waɗanda suke aikata mugunta, mutanen kirki ne a gaban Ubangiji, yana kuwa jin daɗinsu,” kuna kuma cewa, “Ina Allah mai adalci yake?”

  8. Malaki 3:1kusan 397 K.H.

    “Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  9. Malaki 3:2kusan 397 K.H.

    Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki.

  10. Malaki 3:3kusan 397 K.H.

    Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan Ubangiji zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci.

  11. Malaki 3:4kusan 397 K.H.

    Hadayun Yahuda da na Urushalima za su zama yardajje ga Ubangiji, za su zama kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a shekarun baya.

  12. Malaki 3:5kusan 397 K.H.

    “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  13. Malaki 3:6kusan 397 K.H.

    “Ni Ubangiji ba na canjawa. Shi ya sa ku zuriyar Yaƙub, ba a hallaka ku ƙaƙaf ba.

  14. Malaki 3:7kusan 397 K.H.

    Tun zamanin kakanninku, kun juye wa ƙa’idodina baya, ba ku kuma kiyaye su ba. Ku komo gare ni, ni kuma zan koma gare ku,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya za mu koma gare ka?’

  15. Malaki 3:8kusan 397 K.H.

    “Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’ “A wajen zakka da hadayu.

  16. Malaki 3:9kusan 397 K.H.

    Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi.

  17. Malaki 3:10kusan 397 K.H.

    Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  18. Malaki 3:11kusan 397 K.H.

    Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  19. Malaki 3:12kusan 397 K.H.

    “Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  20. Malaki 3:13kusan 397 K.H.

    “Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji Ubangiji. “Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’

  21. Malaki 3:14kusan 397 K.H.

    “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki?

  22. Malaki 3:15kusan 397 K.H.

    A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’ ”

  23. Malaki 3:16kusan 397 K.H.

    Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa.

  24. Malaki 3:17kusan 397 K.H.

    “A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata, za su zama nawa,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima.

  25. Malaki 3:18kusan 397 K.H.

    Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.