- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron.
Sarkin kuma ya lalatar da masujadan kan tuddan da suke gabas da Urushalima, kudu da Tudun Hallaka, waɗanda Solomon sarkin Isra’ila ya gina don Ashtarot, ƙazantacciyar alliyar Sidoniyawa, da Kemosh ƙazantaccen allah na Mowab, da kuma Molek allahn banƙyama na mutanen Ammon.
Yosiya ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya rurrushe ginshiƙan Asheransu, ya baza ƙasusuwan mutane a can.
Har ma da bagaden Betel, masujadan kan tudun da Yerobowam ɗan Nebat ya yi, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi. Wannan bagade da masujadan kan tudun ma ya kawar, ya ƙone masujadan kan tudun, ya niƙa su, ya kuma ƙone ginshiƙin Ashera.
Da Yosiya ya dubi kewaye da shi, ya ga kaburburan da suke can a gefen tudu, sai ya sa aka kwaso ƙasusuwan da suke cikinsu aka ƙone a kan bagade don yă lalatar da shi bisa ga maganar Ubangiji ta bakin mutumin Allah, wanda ya yi annabcin waɗannan abubuwa.
Sarkin ya yi tambaya, ya ce, “Wane kabari ke nan nake gani?” Mutanen birnin suka ce, “Ai, kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuda, shi ne ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.”
Sai ya ce, “Ku rabu da shi, kada wani yă dami ƙasusuwansa.” Saboda haka suka bar kasusuwansa, da na annabin da ya fito Samariya.
Kamar yadda ya yi a Betel, Yosiya ya kawar da dukan ɗakunan gumaka a kan tuddan da sarakunan Isra’ila suka gina a garuruwan Samariya, waɗanda suka tozarta Ubangiji.
Yosiya ya yayyanka dukan firistoci na waɗannan masujadan kan tuddai, ya kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kansu. Sa’an nan ya koma Urushalima.
Sarkin ya ba da umarnin nan ga dukan mutane, cewa, “Ku yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, yadda aka rubuta a Littafin Alkawari.”
Ba a taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa haka ba, tun zamanin da masu shari’a suke aiki a matsayin sarakuna, ko a kwanakin sarakunan Isra’ila, ko na Yahuda.
Amma a shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yosiya, aka yi Bikin Ƙetarewan nan ga Ubangiji a Urushalima.
Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji.
- 2 Sarakuna 23:25kusan 641 K.H.
Babu wani sarki kafin Yosiya, ko kuma a bayansa, wanda ya juya ga Ubangiji da dukan zuciyarsa, da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa bisa ga shari’ar Musa, kamar yadda ya yi.
- 2 Sarakuna 23:26kusan 641 K.H.
Duk da haka, Ubangiji bai huce daga zafin fushinsa wanda ya ƙuna game da Yahuda saboda abin da Manasse ya aikata don yă tozarta shi ba.
- 2 Sarakuna 23:27kusan 641 K.H.
Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan shafe Yahuda ma kamar yadda na shafe Isra’ila, daga gabana, zan ƙi Urushalima birnin da na zaɓa, da wannan haikali wanda na ce, ‘A can Sunana zai kasance.’ ”
- 2 Sarakuna 23:28kusan 641 K.H.
Game da sauran ayyukan mulkin Yosiya, da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
- 2 Sarakuna 23:29kusan 610 K.H.
Yayinda Yosiya yake sarki, Fir’auna Neko, sarkin Masar ya haura zuwa Kogin Yuferites don yă taimaki sarkin Assuriya da yaƙi. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa’ad da Fir’auna Neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Megiddo.
- 2 Sarakuna 23:30kusan 610 K.H.
Bayin Yosiya suka ɗauko gawarsa daga Megiddo suka kai Urushalima, suka binne shi a kabarinsa. Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa.
- 2 Sarakuna 23:31kusan 610 K.H.
Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki. Ya yi mulki na wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna.
- 2 Sarakuna 23:32kusan 610 K.H.
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda kakanninsa suka yi.
- 2 Sarakuna 23:33kusan 610 K.H.
Fir’auna Neko ya sa shi a sarƙa a Ribla a ƙasar Hamat don kada yă yi mulki a Urushalima, sa’an nan ya sa wa Yahuda harajin talenti ɗari na azurfa, da talenti ɗaya na zinariya.
- 2 Sarakuna 23:34kusan 610 K.H.
Fir’auna Neko ya naɗa Eliyakim ɗan Yosiya sarki a maimakon mahaifinsa, ya kuma canja masa suna zuwa Yehohiyakim. Ya ɗauki Yehoyahaz ya kai Masar, a can ya mutu.
- 2 Sarakuna 23:35kusan 610 K.H.
Yehohiyakim ya riƙa biyan Fir’auna Neko azurfa da zinariyar da ya umarta. Don yă yi haka sai ya riƙa karɓar azurfa da zinariya daga mutanen ƙasar, kowa bisa ga ƙarfinsa.
- 2 Sarakuna 23:36kusan 610 K.H.
Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Zebuda ’yar Fedahiya, mutuniyar Ruma.