- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sarakuna 23:37kusan 610 K.H.
Ya kuma aika mugunta a gaban Ubangiji yadda kakanninsa suka yi.
A zamani Yehohiyakim, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasar farmaki, Yehohiyakim dai ya zama abokin tarayyarsa na tsawon shekara uku. Daga baya kuma sai ya canja ra’ayi ya yi wa Nebukadnezzar tawaye.
Ubangiji ya aiki maharan Babiloniyawa, da na Arameyawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa. Ya aike su su hallaka Yahuda bisa ga maganar Ubangiji wadda ya furta ta bakin bayinsa annabawa.
Ba shakka waɗannan abubuwa sun faru da Yahuda bisa ga umarnin Ubangiji domin yă kawar da su daga gabansa saboda zunuban Manasse da dukan abin da ya yi,
haɗe da zub da jinin marasa laifi. Gama ya ƙazantar da Urushalima da jinin marasa laifi. Ubangiji kuwa bai yi niyyar yafewa ba.
Game da sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
- 2 Sarakuna 24:6kusan 599 K.H.
Yehohiyakim ya huta da kakanninsa. Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi.
- 2 Sarakuna 24:7kusan 599 K.H.
Sarkin Masar bai sāke fita daga ƙasarsa don yaƙi ba domin sarkin Babilon ya mamaye yankin, daga Rafin Masar har zuwa Kogin Yuferites.
- 2 Sarakuna 24:8kusan 599 K.H.
Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas da ya zama sarki, ya kuma yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Nehushta ’yar Elnatan, mutuniyar Urushalima.
- 2 Sarakuna 24:9kusan 599 K.H.
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi.
- 2 Sarakuna 24:10kusan 599 K.H.
A wannan lokaci, hafsoshin Nebukadnezzar sarkin Babilon suka kawo wa Urushalima yaƙi, suka kuma kewaye ta.
- 2 Sarakuna 24:11kusan 599 K.H.
Nebukadnezzar na Babilon da kansa kuwa ya zo birnin yayinda hafsoshinsa suka kewaye ta.
- 2 Sarakuna 24:12kusan 599 K.H.
Yehohiyacin sarkin Yahuda, da mahaifiyarsa, da masu yi masa hidima, da hakimansa, da kuma fadawansa duk suka miƙa kansu ga Nebukadnezzar. A shekara ta takwas ta mulkin sarkin Babilon, sarkin Babilon ya mai da Yehohiyacin ɗan kurkuku.
- 2 Sarakuna 24:13kusan 599 K.H.
Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji.
- 2 Sarakuna 24:14kusan 599 K.H.
Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar.
- 2 Sarakuna 24:15kusan 599 K.H.
Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon.
- 2 Sarakuna 24:16kusan 599 K.H.
Sarkin Babilon kuma ya kwashe dukan mayaƙa dubu bakwai, ƙarfafu, shiryayyu don yaƙi, da masu sana’a, da maƙera dubu ɗaya, ya kai Babilon.
- 2 Sarakuna 24:17kusan 599 K.H.
Sarkin Babilon ya sa Mattaniya, ɗan’uwan mahaifin Yehohiyacin, ya zama sarki a madadinsa, ya canja masa suna zuwa Zedekiya.
- 2 Sarakuna 24:18kusan 599 K.H.
Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna.
- 2 Sarakuna 24:19kusan 599 K.H.
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi.
- 2 Sarakuna 24:20kusan 599 K.H.
Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa. To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.
- 2 Sarakuna 25:1kusan 590 K.H.
A rana ta goma ga wata na goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya ne Nebukadnezzar sarkin Babilon tare da dukan rundunan yaƙinsa, ya tasam wa Urushalima. Ya yi sansani a bayan birnin, ya kewaye ta da shirin yaƙi.
- 2 Sarakuna 25:2kusan 590 K.H.
Haka birnin ta kasance a kewaye har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.
- 2 Sarakuna 25:3kusan 588 K.H.
A rana ta tara ta watan huɗu, lokacin da yunwa ta yi tsanani a birnin, babu kuma abinci domin mutane su ci.
- 2 Sarakuna 25:4kusan 588 K.H.
Sai aka huda katanga sa’an nan dukan sojoji suka tsere da dare a ƙofa tsakanin katanga biyu da suke kusa da lambun sarki, ko da yake Babiloniyawa sun kewaye birnin. Suka tsere suka nufi Araba.